Yadda Tsarin Amfani Da Mai Na CNG A Motocinmu Zai Kawo Sauki Maimakon Fetur A Najeriya

CNG

Daga Aminu Bala Madobi

Da ace mutane zasu rungumi tsarin amfani da Compressed Natural Gas (CNG) a motocin su maimakon Fetur, da an samu sauki fiye da yadda ake zato.

Alfijir Labarai ta rawaito an kawo wannan cigaban har da samar da conversion centers a dukkan shiyyoyin kasar nan, mu yan Northwest, an kuma tanadar mana namu a yankin Abuja da jihar Kaduna.

CNG ya fi sauƙi akan fetur da kaso 40 cikin 100, kuma gas ne da baya kamawa da wuta kamar LPG na girki, ba kuma ya hayaki da ke cutarwa, haka kuma akwai arzikin sa a ƙasar nan fiye da yadda ake zato. Akwai buƙatar mutane su rungumi tsarin dan hutawa daga hauhawar farashi da ake samu kan fetur sakamakon yadda kamfanin samar da mai na ƙasa ke fuskantar kalubale kala kala.

Wannan tsarin na CNG yafi sauki, kuma bashi da wata matsala ga ababen hawa. A kwanaki ma naga gwamnati ta cire duty ga duk motar CNG da za a shigo da ita daga ƙasar waje.

Muna da wuyar karɓar sabon cigaba, amma wannan cigaban zai sama mana sauƙi a ɓangaren sufuri da kuma inganta walwalar masu ababen hawa takan kashe kuɗi kaɗan da samun biyan buƙata.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *