Ibtila’i: Wata Sabuwar Gobara Ta Kone Shaguna Kusan 50 m, A Kasuwar Dakata Jihar Kano

IMG 113111 20226 1771583482090

Akalla shaguna 50 ne ake hasashen sun kone sakamakon gobara da ta tashi da asuba a kasuwar Kwalemar Fatima Simra da ke unguwar Dakata, yankin Karamar Hukumar Nassarawa a jihar Kano da safiyar Juma’a.

Shaidun gani da ido sun ruwaito cewar gobarar, wadda aka ce ta fara ne kimanin ƙarfe 5:40 na safe, ta bar ’yan kasuwa suna kididdige asarar su yayin da kaya da dukiya da darajarsu ta kai miliyoyin naira suka salwanta cikin wuta.

Shugaban kwamitin gobarar kasuwar, Dauda Haruna Chula, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da ya yi da ’yan jarida.

Ya bayyana cewa yawancin shagunan da abin ya shafa na kanana ne, wadanda ke harkar sarrafa mai da kuma sake yin amfani da robobi da leda.

A cewarsa, gobarar tana ci gaba da ruruwa a lokacin da yake magana.

“Daga abin da muka gani a farko, kusan shaguna 50 sun riga sun kone, kuma gobarar tana ci gaba. Har yanzu muna jiran jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano,” in ji Chula kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Chula ya kara da cewa jami’an kasuwar sun gaggauta sanar da hukumomin agaji da suka dace da zarar sun lura da tashin gobarar.

“Mun yi iya kokarinmu wajen kiran su da sanar da su halin da ake ciki. Yanzu haka ma ina jin sautin motarsu,” in ji shi.

A lokacin da aka wallafa labarin, ba a tabbatar da adadin asarar gaba daya ba, ko kuma ko akwai wanda ya rasa ransa.

A cewar Daily Trust, wasu ’yan kasuwa a kasuwar sun nuna damuwa kan abin da suka kira jinkiri wajen amsa kira daga hukumomin agaji, suna mai cewa da an yi gaggawa, an rage girman asarar.

Baka iya gana komai a yanzu haka sai hayaki, da ya turnuke kasuwar da Kuma sararin samaniya. ‘Yan kasuwa sun yi dandazo.

Kasuwa ce da ake sarrafa gyada don samar da mankuli. Rumfuna da Na’urori da dama sun kone.” Inji Wakilin Justice Watch Hausa.

Annobar ta faru ne bayan mako guda da gobara ta tashi a kasuwar Singer da ta shafi ’yan kasuwa fiye da 1,000 a jihar Kano.

Sai dai hukumomi ba su fitar da sanarwar hukuma ba kan wannan sabon lamari yayin da bincike kan musabbabin gobarar ke ci gaba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *