Ibtila’i: Yan wasan kungiyar Kano Pillars sun gamu da haɗari a Jos

FB IMG 1729622534913

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekaru 19 na Kano Pillars ta yi haɗari a garin Jos.

Tawagar ta yi haɗarin ne a hanyarsu ta zuwa filin wasa na Jos domin buga wasa a gasar matasa ta ‘yan kasa da shekaru 19.

Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da sashin yada labarai na kungiyar ya fitar a yau Talata.

“Muna bakincin sanar da cewa, motar da ke dauke da tawagar U-19 ta Kano Pillars FC ta yi hatsarin mota a yau, yayin da take kan hanyarta zuwa Sabon Filin Wasa na Jos don buga wasan cikon mako na 5 a gasar matasa ta U-19 da Plateau United .

“Wasu daga cikin ‘yan wasan da direban sun ji rauni a wannan mummunan al’amari, kuma an gaggauta kai su asibiti don samun kulawar likitoci.

Sai dai Alhamdulillahi, ba a samu asarar rai ba a wannan lokaci, kuma tawagar likitocin na ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki.”

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *