Ibtila’i: ‘Yanbindiga sun kashe mutum 50 da garkuwa da wasu da dama a Jihar Zamfara.

IMG 221336 21226 1771708440659

Aƙalla mutane 50 ne suka mutu yayin da aka yi garkuwa da mata da yara da dama a wani hari da aka kai wani ƙauye a Jihar Zamfara a Nijeriya.

Harin, wanda ‘yan ta’adda da ake kira ‘yan bindiga a yankin suka kai, ya fara ne a daren Alhamis kuma ya ci gaba har zuwa safiyar Juma’a.

Maharan da suka iso a kan babura sun banka wa gine-gine wuta tare da harbin mazauna ƙauyen Tungan Dutse da suka yi ƙoƙarin tserewa, kamar yadda Hamisu Faru, ɗan majalisar jiha, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu a ranar Asabar.

“Tun daga daren Alhamis har zuwa safiyar yau babu wanda ya samu barci. Wasu mutane sun rasa ‘yan uwa uku daga cikin iyalansu,” in ji Faru ga Anadolu.

An shirya gawawwakin waɗanda suka mutu domin jana’izar gama-gari, inda aka lulluɓe su da farin likkafani a ranar Asabar. Har yanzu ba a tantance adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba, yayin da jami’an yankin ke ci gaba da ƙididdige waɗanda suka ɓace.

TRT Hausa

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *