Ilimi! An gano makaranta mai ɗalibai 1,200 amma malamai 8 ne kacal ke koyarwa a Kano

Makaranta

Makarantar Sakandaren gwamnati ta Rufa’i  Tudun Wada da ke karamar Hukumar Doguwa, wacce ita ce karamar makarantar sakandare daya tilo a yankin, na da ɗalibai 1,200 amma malamai 8 kacal ke koyarwa a makarantar.

A wani bincike da jaridar DAILY POST ta yi, makarantar na da malamai na dindindin guda uku kawai sai kuma malaman sa-kai guda biyar, wadanda ke fafutukar kula da yawan daliban.

Binciken ya gano cewa a halin yanzu, makarantar na da rukunin ajujuwa biyu kacal, yayin da na ukun ya lalace, ba zai amfanu ba.

Wakilin jaridar ya kuma ruwaito cewa, ’yan kasuwa sun ciyo harabar makarantar, inda har ake sayar da bulo a farfajiyar makarantar.

Wakilin DAILT POST, wanda ya ziyarci yankin a wani bangare na binciken yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aiwatar da shirin bada agajin gaggawa kan ilimi na jihar, ya lura da cewa ana gina sabon rukunin ajujuwa amma ginin ya tsaya ko bai yi nisa ba.

Shamsuddeen Haruna, wani malamin sa kai wanda ya kwashe shekaru takwas ya na hidima a makarantar, ya bayyana cewa himma da jajircewarsa ga al’ummarsa ne suka sa ya ci gaba da koyarwa duk da mawuyacin hali.

Daily Nigerian

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *