Inda Ba Kasa! Gwamnatin Najeriya Ta Maka Gwamnonin Kasar 36 Kara A Gaban Kuliya

IMG 20240527 WA0016

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamnatin tarayya ta dau matakin shari’a a kan gwamnonin jihohin tarayya 36, ​​inda ta gurfanar da su a gaban kotun koli bisa zargin yin katsalandan a harkokin kananan hukumomi.

Alfijir labarai ta rawaito Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN, ne ya shigar da karar, wanda ke neman a ba kananan hukumomi cikakken ‘yancin cin gashin kansu a matsayin mataki na uku a gwamnatin kasar.

A cikin karar mai lamba SC/CV/343/2024, AGF tana neman umarnin kotun koli da ta haramtawa gwamnonin jihohi rusa kananan hukumomin da aka zaba ba bisa ka’ida ba. Manufar ita ce a tabbatar da cewa an gudanar da kananan hukumomi bisa cin gashin kansu ba tare da tsangwama daga hukumomin jihohi ba.

Babban lauyan gwamnatin a cikin sammacin da ya nema, ya kuma roki kotun koli ta bayar da umarnin ba da izinin shigar da kudaden da ke cikin asusun kananan hukumomi kai tsaye zuwa gare su daga asusun tarayya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.

Ya kuma bukaci kotun koli ta ba da umarnin dakatar da gwamnonin kafa kwamitocin riko da za su tafiyar da al’amuran kananan hukumomi sabanin yadda tsarin mulkin kasar ya amince da kuma ba da tabbacin dimokuradiyya.

Hakazalika ta nemi a ba da umarnin hana gwamnoni da wakilansu da masu zaman kansu karba, kashewa ko kuma tafka magudin kudaden da aka fitar daga asusun tarayya domin amfanin kananan hukumomi a lokacin da ba a samar da tsarin kananan hukumomi na dimokuradiyya ba.

Gwamnonin Jihohin 36 sun kai kara ne ta hannun manyan Lauyoyin su.

“Tsarin mulkin Najeriya ya amince wa gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi a matsayin su na matakai uku na gwamnati sannan kuma aka amince da su suna fitar da kudade don gudanar da ayyukansu daga asusun tarayya da kundin tsarin mulki ya kirkiro.

“Cikin tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki, dole ne a samar da tsarin kananan hukumomi na dimokuradiyya, kuma kundin tsarin mulki bai yi tanadin wasu tsare-tsaren gudanar da mulki a matakin kananan hukumomi ba sai na kananan hukumomi da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya.

“Cewa gazawar da gwamnonin suka yi wajen aiwatar da tsarin kananan hukumomi na dimokuradiyya, rusa kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ne da gangan wanda su da shugaban kasa suka sha alwashin tabbatar da su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/F9mRRuOf58G3MlLKsNCJbL

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *