
Alfijr ta rawaito INEC ta sanya ranar Asabar 15 ga watan Afrilu a matsayin ranakun da za ta kammala zabukan da ba a karasa ba a kasar.
Rotimi Lawrence Oyekanmi, babban sakataren yada labarai na shugaban INEC ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin.

Baya ga wannan, a wani sako da hukumar ta kuma wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta yanke shawarar ne bayan wata ganawa da ta yi da jami’an hukumar a wannan Litinin din.

Hukumar ta saka ranar Asabar 15 ga watan Afrilun ne, za a karasa zabukan gwamnoni da na ’yan majalisun dokokin da ba a karasa ba, sakamakon wasu matsaloli.
Idan zaku tuna, INEC dai ta ayyana zabukan gwamnonin jihohin Adamawa da Kebbi a matsayin wanda bai kammala ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇