Innalillahi wa inna ilaihirraji un Gobara ta kone Alibert Furniture dake Hadejia Road a Kano

Innalillahi wa inna ilaihirraji un 
Gobara ta kone Alibert Furniture dake Hadejia Road a Kano

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

 Wani Katafaren kamfani ne da ke Kano, Alibert Furniture, ya kone kurmus a jihar.

 Gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar Litinin, inda ta kona kamfanin da ke kan hanyar Murtala Mohammed daga kano. 

Wata majiyar ta sanar damu  cewa jami’an tsaro biyu na kamfanin sun samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su asibiti. 

Duk da cewa har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, shaidu sun alakanta gobarar da matsalar wutar lantarki da ta samu daga na’urar taranfoma da ke kamfanin. 

Best Seller Channel 

Jami’an kwana-kwana sun yi nasarar kashe gobarar amma har yanzu wasu sassa na ginin na ci da wuta lokacin  hada wannan rahoto.

Allah ya kiyaye faruwar haka a nan gaba ameen. 

Allah ya mayar da abinda aka rasa ameen summa ameen. 

Slide Up
x