Innalillahi wa inna ilaihirraji un ! Mutane da Dama Sun Mutu a Wani Hatsarin Mota a Hanyar Bauchi Zuwa Jos

Innalillahi wa inna ilaihirraji un ! Mutane da Dama Sun Mutu a Wani Hatsarin Mota a Hanyar Bauchi Zuwa Jos

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

Mutane da dama ne suka mutu a wani mummunan hatsarin da ya afku a ranar Alhamis a kan hanyar Bauchi zuwa Jos. 

Jaridar Punch ta ruwaito,cewa har yanzu ba a kai ga tantance adadin wadanda suka mutu a hadarin ba, hotunan da aka aiko daga inda lamarin ya faru ya nuna gawarwaki hudu kwance a kasa. 

A cewar rahotanni, Motar Hummer Bus da Sharon Bus ne suka yi taho mu gama.

 An gano cewa daya daga cikin motocin da lamarin ya shafa ta kama wuta kuma tana ci gaba da konawa har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Best Seller Channel 

 Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya reshen jihar Bauchi Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu a wata tattaunawa ta wayar tarho. 

Sai dai ya ce har yanzu ba a san adadin wadanda suka mutu ba.

 Hukumar kiyaye haddura ta jihar Bauchi Yusuf Abdullahi ya tabbatar wa wakilinmu afkuwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho. 

Sai dai ya ce har yanzu ba a san adadin wadanda suka mutu ba. “Eh, an samu wani hatsari da yammacin yau a kewayen garin Buzaye da ke kan hanyar Bauchi zuwa Jos. 

Best Seller Channel 

A yayin da nake magana da ku, ana ci gaba da gudanar da aikin ceto a wurin da hatsarin ya afku. 

Don haka, ba zan iya gaya muku ainihin adadin mutanen da aka kashe ba. 

Bayan aikin ceto, zan yi muku cikakken bayani,” in ji Abdullahi.

Slide Up
x