Shugaban ƙasar Masoud Pezeshkian ya bayyana sharudda uku da Iran ta ce dole a cika kafin a kawo ƙarshen yaƙin da Amurka-Isra’ila suka kaddamar a kanta.
A wata sanarwa daya wallafa, Pezeshkian ya ce Iran na goyon bayan zaman lafiya, amma ya jaddada cewa ba za a iya kawo ƙarshen yaƙin ba sai an cika wasu muhimman sharuɗɗa.
Ya ce sharuddan sun haɗa da:
1. Amincewa da haƙƙoƙin Iran a matakin ƙasa da ƙasa.
2. Biyan diyya ga Iran kan asarar da ta yi sakamakon hare-haren da aka kai mata.
3. Samar da tabbacin ƙasa da ƙasa da zai hana sake kai mata hare-hare a nan gaba.
Shugaban ya kuma bayyana cewa Iran na da niyyar ganin an samu zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, amma ya zargi Amurka da Isra’ila da haddasa rikicin da ake fama da shi a yanzu.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t