Iyalan ’Yan Sandan Da Suka Mutu A Bakin Aiki A Zamfara An Gwangwaje su da N5.1m
Da yake gabatar da cakin kudin ga iyalan mamatan, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ayuba Elkanah, ya ce an mika musu tallafin ne domin su rage radadin rayuwar rashin ’yan uwana suka yi .
Kwamishinan ya ce tallafin ya zo ne a lokacin da aka fi bukatarsa, kuma zai dada zaburar da sauran jami’an da suke aiki don jajircewa.
Jaridar Aminiya ta rawaito Babban Sufeton ’Yan Sanda, Usman Alkali Baba, ya damu matuka da walwalar jami’ansa, musamman a bangaren biyan inshorar rayuwa da sauran hakkokin wadanda suka mutu a bakin aiki.
Daga nan sai ya shawarci iyalan mamatan da su yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace, yana mai cewa rundunar a Jihar ta gabatar da makamancin wannan tallafin ga iyalan jami’anta da dama da suka rasu a baya.
Daya daga cikin iyalan mamatan, Usman Musa, wanda ya karbi Naira miliyan uku da dubu dari da sittin, a madadin dan uwansa, ASP Dankane S Rafi, ya mika godiyarsa ga Babban Sufeton.
Allah ya taimaki masu taimakon mabukata amin.