Wata Dalibar B U K Ta Rasu A Hostel

Wata dalibar BUK ta mutu a hostel. 

Dalibar yar level 400 daga tsangayar Education ta Jami’ar Bayero Kano Binta Isa ta rasu a dakin kwananta a ranar Juma’a 26 ga watan Nuwamba bayan rashin lafiya. 

KANO FOCUS ta ruwaito cewa marigayiyar wanda ta fito daga jihar Kogi, ta rasu ne da misalin karfe 7 na dare bayan da ta yi korafin ciwon kirji. 

A cewar daraktan sashen kula da lafiya na jami’ar, wanda ya ce marigayiya Binta Isa ta taba zuwa asibitin New Campus, a ranar Laraba, 24 ga watan Nuwamba, inda ta koka da ciwon kirji aka yi mata gwaji da bata wasu magunguna.

Daraktan ya kuma bayyana cewa marigayiyar ta cigaba da halartar laccocinta a ranakun Alhamis da Juma’a, da kuma sauran ayyukan da ta saba yi. 

A ranar Juma’a 26 ga watan Nuwamba da yamma lokacin sallar magriba ta sake kokawa abokan zamanta da ciwon  kirji amma ta samu ta dauro alwala ta yi sallar magriba a dakin. 

Sai dai abokan zaman da suka dawo suka tarar da ita a kwance. 

Nan take suka sanar da mahunta aka kai ta asibitin koyarwa na Aminu Kano inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta. 

Mataimakin shugaban jami’ar Sagir Adamu Abbas tare da magatakardar jami’ar Jamil Ahmad Salim da daraktan kula da lafiya na jami’ar da kuma daraktan tsaro Abdulyakin Ibrahim duk sun halarci wurin. 

Wata sanarwa da mai magana da yawun jami’ar Lamara Garba ya aike wa KANO FOCUS a ranar Asabar ta ce hukumar gudanarwar jami’ar ta tuntubi dan uwanta da ke zaune a Kano game da lamarin. 

Mataimakiyar shugabar jami’ar, a madadin hukumar gudanarwa, ma’aikata da daliban jami’ar, ta bayyana alhinin ta dangane da rasuwar matashiyar Binta Isa, wadda ta rasu a lokacin da take taka muhimmiyar rawa a karatun ta. 

Ya mika sakon ta’aziyya ga iyayenta da ‘yan uwa da abokan aikinta. Yayi addu’ar Allah ya gafarta mata gajeran Allah ya kyautata zuwanta, ya kuma sa Aljannar Firdausi ce makomarta