Jagororin Gwamnatin Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar Sun Naɗa Ministoci

Daga Aminu Bala Madobi

Jagororin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun nada sabbin ministoci a sabuwar gwamnati.

Alfijir Labarai ta rawaito cikin wata doka da aka karanta a gidan talabijin na kasar a ranar Alhamis, ta tabbatar da wannan ci gaban.

Firayim Minista Ali Mahaman Lamine Zeine ne zai jagoranci gwamnati mai mambobi 21, tare da janar-janar sabuwar majalisar mulkin sojan da ke jagorantar ma’aikatun tsaro da na cikin gida.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin kasashen yammacin Afirka za su gana a yau Alhamis domin yin tir da matakin soji kan gwamnatin mulkin soji, karkashin jagorancin tsohon kwamandan tsaron shugaban kasar, Janar Abdourahmane Tchiani.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *