Kotun sauraron korafin zabe ta soke zaben Hon Mukhtar Yarima a matsayin Dan majalisar tarayya mai wakiltar Tarauni.
Alfijir Labarai ta rawaito Kotun mai Alkalai 3, ta tabbatar da Hon Hafiz Ibrahim Kawu na Jam’iyyar APC a matsayin wanda lashe zaɓen kuma ta tabbatar da kujerar gare shi, bisa dogaro da hujjar gabatar da sakamakon bogi na makarantar Firamare da Dan majalisar Yarima yace yayi.
Yarima dai ya tsaya ne karkashin inuwar Jam’iyyar NNPP a zaben da akayi a watan Fabarerun daya gabata.
Jim kadan bayan fitowa daga kotun, lauyan Mukhtar Yarima Barista Rabiu Sadiq yace sun karbi wannan hukunci kuma zasu daukaka kara.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI
Wannan saka mako yayi kyau
Zancen banza, mutane sun zabi abinda sukeso amma kotu zatayi musu fashi