JAMB Ta Bankaɗo Ɗalibai 3000 Da Suka Kammala Karatun Bogi A Najeriya

FB IMG 1720123142515

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB), ta bankaɗo dalibai 3000 da suka kammala karatun bogi, wadanda ba su taba taka kafa a aji don ɗaukan karatu ba.

Alfijir labarai ta ruwaito hukumar ta kuma yi Allah wadai da yadda wasu makarantu ke bayar da gurbin karatu ba bisa ka’iɗa ba, wanda a cewarta, hakan na ci gaba da zama abin kunya ga kasar nan.

Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne, ya sanar da hakan ga shugabannin kwamitin kula da jami’o’in kamar rahoton da hukumar ya tabbatar.

A watan Disambar 2023, Kwamitin majalisar wakilai mai kula da ilimin bai daya ya umarci hukumar JAMB da ta gabatar da jerin sunayen manyan makarantun da suka gudanar da jarabawar shiga jami’a ba bisa ka’ida ba.

A baya dai hukumar jarabawar ta gargadi ɗalibai da su guji karbar gurbin karatu ko shaidar kammala karatu daga irin waɗannan jami’o’in da ke bayar da shaida ba tare da cikakken halartar karatu ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *