Alfijr ta rawaito wani matashi mai shekaru 21 mai suna Micheal Arigbabuwo ya rasa ransa a wurin bikin zagayowar ranar haihuwarsa bayan da aka zarge shi da zuba kwayoyi cikin abin shansu domin samun nutsuwa.
Alfijr Labarai
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Lagos SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da hakan a cikin tabbataccen shafin sa na Twitter a ranar Lahadi.
Hundeyin ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a unguwar Ikorodu da ke Lagos, inda ya jaddada cewa an kama abokansa uku wadanda da su aka shirya komai.
Kakakin ya ce bayanan da ‘yan sanda sun sami kiran gaggawa a unguwar Ikorodu da misalin karfe 7:30 na dare.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka samu wani kira na nuna damuwa cewa wasu ’yan kungiyar Yahoo Yahoo sun kawo gawa zuwa yankin Igbogbo da ke Ikorodu.
Alfijr Labarai
“Bisa bayanin, Jami ansu na sirri sun gudanar da binciken yayin da suka ziyarci inda lamarin ya faru.
Ya kara da cewar, an kama wasu matasa uku masu shekaru 23 da 24. “Wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewa marigayin ya sha codeine da tabar wiwi, a wajen bikin zagayowar ranar haihuwar daya daga cikin abokansu da aka gudanar a yankin Igbogbo a Ikorodu.
“Wadandanda ake zargin sun kara da cewa marigayin ya fara haki ne, sa annan aka garzaya da shi asibiti, inda a can ya mutu,” inji su.
Kakakin ya ce an kai gawar an ajiye ta a babban asibitin Ikorodu domin a tantance gudanar da binciken kwakwaf.
Hundeyin ya gargadi matasa kan shaye-shayen miyagun kwayoyi, inda ya jaddada cewa, miyagun kwayoyi za su kawo karshen rayuwarsu cikin bala’i.
Saka kai cikin mu amula da kwayoyi a kwai babbar illa, babu wani abu cikinta sai da na sani.
Ya rufe da cewar, an cigaba da bincike kan lamarin,” in ji shi.
NAN