Alfijr ta rawaito Jami’an Tsaro na Yan sanda a Jihar Kano sun Gayyaci zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Dala ta Jihar Kano a jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP, Aliyu Madaki

Kakakin Rundundar yan sandan jihar ta Kano SP Abdullahi Haruna kiyawa ya Tabbatar da Tsare Honourable Aliyu Sani Madakin Gini.
Ya kuma tabbatar da cewa ana gudanar da bincike daga Sashin kula da bincike na rundundar yan sandan jihar ta Kano dake Bompai

Ana tuhumar Madakin Gini da yin amfani da bindiga yayin Gangamin yaƙin neman zabe, wanda hakan ya Saba da Doka.
Kawo yanzu dai Yana Ci gaba da kasancewa a shelkwatar Yan sandan kafin samun sanarwa ta Gaba
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇