Jami’an Tsaron Farin Kaya DSS Sun Damƙe Sanata Yari

DSS sun kama wani tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari tare da tsare shi tsawon dare biyu.

Alfijir Labarai ta rawaito an kama Yari ne bayan kiran wayar tarho da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi a watan da ya gabata a kan shugaban majalisar dattawan kasar.

Wani babban jami’in tsaro da kuma mai taimaka wa gidan gwamnatin jihar ya bayyana cewa hukumar DSS ta kama Yari a safiyar ranar Alhamis tare da tsare shi saboda “tunanin shugaban kasa abin wasa ne,” kamar yadda wani jami’in ya bayyana.

“An tambaye shi dalilin da ya sa ya yi watsi da kiran wayar shugaban kasa yayin neman kujerar shugabancin majalisar dattawa,” in ji wani jami’in.

“Ya fara jayayya cewa yana da cikakken ‘yancin tsayawa takara kuma yanke shawara kan harkokin siyasar sa bai kamata ya fito daga shugaban kasa ba.

“Shugaban kasa yana kokarin rokonsa da ya janye aniyarsa ta ganin ba za a sake komawa ga duk wata kaddara irin ta yadda Bukola Saraki ya zama shugaban majalisar dattawa a 2015 ba.

“Dukkanmu mun san cewa bayyanar Saraki a wancan lokacin ita ce kuskuren farko da shugaba Buhari ya yi, kuma hakan ya gurgunta shekaru hudu na farko a kan karagar mulki,” in ji jami’in ya shaidawa Gazette.

Majiyoyi sun ce Yari ya samu kira daga Yusuf Bichi, babban daraktan hukumar DSS, da ya kawo rahoto a hedikwatar hukumar domin tattaunawa cikin gaggawa.

Da isar tsohon gwamnan ne aka bukaci ya jira Bichi, wanda aka ce ya fita.

Amma Sanatan yayi ta jira a tsawon ranar tare da wasu gungun jami’an ‘yan sanda dauke da makamaii, sai da misalin karfe 10:00 na dare aka sanar masa sai hobe Alhamis ba zai koma gida ba.

A sakamakon haka ne aka dakatar da ziyarar da Yari da wasu takwarorinsa na Majalisar Dattawa suka yi wa tsohon Shugaban kasa Ibrahim Babangida a ranar Juma’a.

Majiyar ta kara da cewa “An kwace wayoyinsa, kuma yana iya yin kwanaki a tsare.

An tattaro cewa an kuma tambayi Yari game da hada-hadar da ya samu daga babban bankin Najeriya (CBN), wanda jami’ai ke daukarsa a matsayin abin tuhuma amma Sanatan ya bayyana cewa halas ne.

Wata majiya ta ce “Ya ce musu kudaden da CBN suka samu daga kwamitin tuntuba da ya yi wa taron gwamnoni ne kuma har yanzu yana da ma’auni da zai iya karba daga CBN.”

Peoples Gazette

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *