Jam’iyyar PDP ta yi zazzafan martani ga kalaman Ganduje

Ganduje

Kai da ka kasa cin zabe a jihar Kano, ta yaya zaka iya bai wa APC nasara a Kudu Maso Yamma.

Alfijir labarai ta rawaito Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Osun, Mista Sunday Bisi, ya gargadi Shugaban APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, da ya guji yin furucin da zai iya tayar da tarzomar siyasa a yankin Kudu maso Yamma.

Bisi, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, yana martani ga kalaman da Ganduje ya yi a wajen taro  a Jihar Ondo, inda aka rawaito ya ce jam’iyyarsa na da dabarar “mamaye” dukkanin yankin Kudu maso Yamma.

Shugaban PDP ya gargadi Ganduje cewa irin wadannan kalaman na iya tayar da hankulan jama’a da haifar da rashin zaman lafiya a kasar. Ya kuma jaddada cewa mutanen Osun za su yanke hukunci kan wanda zai mulke su idan lokacin ya yi.

Yayin da yake bayyana kalaman Ganduje a matsayin “kokari na jefa yankin Kudu maso Yamma cikin rikicin siyasa da ba ya da amfani,” Bisi ya gargadi cewa Najeriya, da tuni take fama da rikice-rikicen kabilanci da kalubalen tattalin arziki, bai kamata a kara tayar mata da hankali ba.

Sunday ya ce, “Ga mutum wanda bai iya cin zabe a  jiharsa ta Kano ba,  saboda rashin iya mulki a wa’adinsa a matsayin gwamna, ya zo yanzu yana barazanar zuga yankin Kudu maso Yamma da wuta da hayaki ba kawai rashin hankali ba ne, amma rashin tunani ne kwata-kwata.

“Yayin da Shugaban Kasa ke ci gaba da fuskantar matsalar tattalin arzikin kasar, Ganduje ya kamata ya yi taka-tsan-tsan kada ya kara dagula lamarin ta hanyar kokarin yin magudi a zaben, musamman a yankin Kudu maso Yamma. Yin hakan zai zama tamkar taka kan maciji mai hadari.

“Idan Mallam Ganduje ya kasa, kamar yadda ya yi, wajen tayar da rikici a Kano, inda aka yi watsi da APC saboda mulkinsa mai tsanani, ya kamata ya shirya karbar irin wannan sakamakon a wasu jihohin da APC ta kasa gamsar da masu zabe.”

Daily Nigerian

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *