Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da neman Kwamishinan Aiyuka na Musamman, Auwalu Danladi Sankara ruwa a jallo bisa zargin sa da neman matar aure.
Alfijir labarai ta rawaito cewa Hisbah ta kama tare da tsare Sankara a makon da ya gabata bayan da mijin matar ya shigar da korafi cewa Kwamishinan na neman matar sa.
Amma daga baya Hisbah ta bada belin Sankara ta hannun wani Ahmed Dantata, kamar yadda shigaban Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a taron manema labarai da ya kira a ranar Litinin.
A cewar Daurawa, an yi da Sankara cewa zai zo shelkwatar Hisbah a yau domin a saurari ɓangarorin da kuma yadda za a yi sulhu.
, “amma gashi har yanzu bai zo ba kuma bai turo wakili ba. Lauyan É—aya bangaren ga shi can ya zo amma shi har yanzu shiru.
“Shi ya sa mu ke sanar da Æ´an jarida cewa mu na neman sa ruwa a jallo. Wanda ya tsaya masa ma yai belin sa shima muna neman sa kuma za mu gabatar da su a kotu,” in ji Daurawa.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj