Alfijr
Alfijr ta rawaito rundunar Ƴan Sandan jihar Kano tace ta samu nasarar kama ƴan daba 84 da muggan makamai a yayin bukukuwan sallah babba a faɗin jihar.
Kwamishinan Ƴan sanda na jihar Kano, Samaila Shu’aibu Dikko ne ya bayyana kama ƴan daban ne a fadin jihar a yayin bukukuwan Sallah, kamar yadda mai magana da yawun hukumar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Juma’a
Alfijr
SP Kiyawa ya ƙara da cewa ƴan daban sun shiga hannu ne a ranakun Hawan Daushe da Hawan Nasarawa da Hawan Dorayi da sauran haye-hayen Sallah da aka yi a sauran masarautun jihar 5.
A sanarwar, kwamishinan ya yabawa al’ummar jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki akan tsaro bisa gudunmawar da su ka bayar har aka samu gagarumar nasara a yayin bukukuwan Babbar Sallah.
Alfijr
Kiyawa kara da cewa za a iya tuntuɓar rundunar domin kiran gaggawa a kan waɗannan lambobin waya:
08032419754, 08123821575, 08076091271 09029292926.