Jihar Kano Ta Samu Gurabe Masu Tsoka A Aikin Hajjin Bana

Alfijr ta rawaito hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta baiwa Jihar Kano gurbin alhazai dubu 5902 domin zuwa aikin Hajjin bana, 2023.

Muhammad Abba Dambatta wanda ke zaman Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ne ya bayyana hakan a yau Asabar yayin ƙaddamar da shirin bita na wannan shekara a Kano.

Sakataren ya ce tuni kimanin maniyyata dubu 4 ne suka biya kudin ajiya.

Ya kara da cewa ce gwamnatin jihar ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin an gudanar da ayyukan Hajjin da ke tafe ba tare da tangarda ba.

Ya ce hatta aikin Hajjin bara da aka samu matsaloli, jihar Kano ta taka rawar gani inda wanda ya kai ga samun lambobin yabo da dama musamman daga ƙungiya Hajj Reporters.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *