Kamfanin BUA Ya Gina asibiti, Makaranta Da Masallaci Na Naira Miliyan 280 A Sakkwato

Alfijr ta rawaito kamfanin siminti na BUA a ranar Laraba 3/8/2022 ya mikawa al’ummar Gidan Boka da ke Ƙaramar Hukumar Wamakko wani asibiti da makaranta da masallaci, da kudinsu ya kai Naira miliyan 280.

Kamfanin ya danƙa gine-ginen, wanda tuni aka kammala, har da tagomashin ton 170 na siminti ga al’ummomi 68 a karamar hukumar.

Manajan Daraktan Kamfanin Simintin na BUA, Yusuf Binji, ya ce wannan karamcin wani bangare ne na alhakin yi wa al’ummar da kamfanin ya ke alheri.

Alfijr

Daraktan Ma’aikata na BUA, Altine Wali a madadin Yusuf Banji, ya ce kamfanin ya gudanar da aikin samar da matsugunan ne a wani bangare na shirin fadada katafaren gini, tare da share filaye a cikin al’ummar Gidan Boka da kuma raba filaye ga iyalan da abin ya shafa.

Da yake jawabi, shugaban gudanarwa da ayyuka na kamfanin, Sada Suleiman, ya ce kamfanin ya kuma gina tituna, da kuma samar da makabarta, ruwan bututu da wutar lantarki ga al’umma.

Alfijr

Ya ce, kamfanin ya tabbatar da shirin raba siminti ga al’umma domin gyara masallatai da sauran ababen more rayuwa, da kuma samar da magunguna da sauran kayayyakin masarufi ga ‘yan kasa a cikin al’ummomin yankin.

“Kamfanin Simintin BUA yana tallafawa al’ummomin a fannin kiwon lafiya, horar da basira, samar da guraben karatu da kayan ilimi,” in ji shi.

Kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa

Slide Up
x