Karancin Fetur Da Sake Fasalin Naira Duk Makirci Ne Akan Takarata-Tinubu

Alfijr ta rawaito Bola Ahmed Tinubu ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, a ranar Laraba ya yi zargin shirin yin magudi a zaben 2023 ta hanyar karancin man fetur da sake fasalin Naira.

Tinubu yayi magana ne a Abeokuta, jihar Ogun, yayin yakin neman zabensa. T

Ya sha alwashin cewa ‘yan Najeriya za su bijirewa karancin man fetur da kuma tattaki domin kada kuri’a.

Ya ce zabukan da ke tafe za su kasance mafi girman juyin juya hali.

“Ba sa son a gudanar da wannan zabe.

Suna son yi mana zagon kasa a zaben.

Shin za ku kyale su”,

Tinubu ya tambayi magoya bayan da suka hallara a wurin taron, inda suka amsa da “A’a.”

Sai dai ya sha alwashin cewa ‘yan Najeriya za su bijirewa matsalar karancin mai da kuma tattaki domin kada kuri’unsu.

Tinubu ya sha alwashin cewa “za mu yi amfani da PVC mu karbe gwamnati daga hannunsu,” kamar yadda ya nuna cewa zabe mai zuwa zai zama “juyin juya hali.”

“Ko da sun ce babu mai, za mu yi tattaki don kada kuri’a.

Suna da ɓarna da yawa; suna iya cewa babu mai. Sun dade suna kulla makarkashiyar haifar da matsalar man fetur, amma ka manta da su.

“Ku kwantar da hankalinku, ni, Asiwaju, na gaya muku cewa za a magance matsalar samar da mai har abada.

Duk wanda yake so ya ci zumar da ke cikin dutse ba zai damu da gatari ba.

Ashe ba haka bane Kuma idan ana son cin dabino, sai a kawo dutse a yi amfani da shi wajen karya shi, sai kwaya ta fito.

Ya Kara da cewar, ba abu ne mai sauki ba…

“A bar su su kara kudin man fetur, su kadai suka san inda suka tara mai, sun tara kudi, sun tara Naira; za mu je mu zabe mu kuma za mu yi nasara.

Ko da sun canza tawada a takardun Naira, komai shirinsu zai lalace, za mu yi nasara, wadanda ke PDP za su yi rashin nasara. In Ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *