Karshen Tuka-Tuki! Bayan Caka Wa Wata Budurwa Wuka Ya Kwace Mata Waya! Ya Shiga Hannu

IMG 20240503 WA0010

Barawon da ya caka wa wata budurwa wuka ya kwace wayarta a garin Damaturu na Jihar Yobe ya fada komar ’yan sanda.

Alfijir Labarai ta rawaito kwanakin baya wani barawon waya ya kwace wayar budurwar bayan da ya caka mata wuka a gidan baya a unguwar Malari a garin Damaturu fadar.

Sakamakon haka aka garzaya da ita babban Asibitin koyarwa na jihar inda a halin yanzu take samun kulawa.

A wata sanarwa, kakakin ’yan sandan jihar ta Yobe, ASP AbdulKareem Dungus ya ce jami’an su sun kama matashin.

Kotun Abuja ta ɗage shari’ar jami’an Binance
An tsinci gawar wata ɗaliba a cikin ɗaki a Kano
A cewarsa, wayar da barawon ya kwace samfurin Itel ce hade da da layi a ciki.

Dungus ya ce za a ci gaba da bincike daga bisani a tura matashin zuwa kotu don fuskantar hukuncin da ya ya daidai da laifinsa, domin hakan zama izina ga na baya.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *