Daga Aminu Bala Madobi
Karamin ministan tsaro Dr. Bello Matawalle ya bayyana bacin ransa kan yadda ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga ke cin karensu ba babbaka a jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina da Kebbi da kewayen su.
Alfijir Labarai ta rawaito karamin ministan ya umarci manyan hafsan hafsoshin tsaro da sauran hafsoshin soji da su koma sokoto.
Wannan mataki na nuna irin jajircewar da gwamnati ta keyi na maido da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Yayin da a yankin Arewa maso Yamma jami’an za su kula da ayyuka da kuma tabbatar da an fatattaki Bello Turji da ’yan tawagar sa.
Wadannan ’yan fashi da makami sun yi ta yada wani bidiyon wata mota mai sulke ta sojojin Najeriya da ta makale a wani wuri mai cike da ruwa kuma da daddare, inda aka bukaci jami’an da su janye don gudun kada ‘yan fashi su yi musu kwanton bauna, daga bisani kuma cikin dare ‘yan fashin suka je wurin ruwan, suka nadi bidiyon motar sulken da ta makale sunata shewar bikin samun nasarar ta.
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a Henshaw Ogubike ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar
Ya ce wannan lamari ya faru ne a kwashabawa da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.
Ya kuma ce hakan ba abu ne da za a amince da shi ba, kasancewar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu GCFR yana bayar da gagarumin goyon baya ga rundunar sojin Najeriya don yakar ‘yan taadda.
Ya ci gaba da cewa, Gwamnatin Tarayya ta damu matuka game da barazanar ‘yan bindiga da ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma musamman.
“Lokaci yayi na yakar wadannan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda saboda karuwar ayyukan da aka saba yi za su raunana dukkan sansanonin su.”
Matawalle ya kuma tabbatar wa al’ummar jihohin Sakkwato da Katsina da Zamfara da Kebbi da kuma yankin Arewa maso Yamma baki daya cewa jami’an tsaro ba za su bar wani abu ba har sai sun fatattaki ‘yan bindigar.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj