Kasar Saudiyya Ta Haramta Jirgin Najeriya Shiga Kasar, Kan Cutar Corona Omicron

 Da Dumi Duminsa. 

Kasar Saudiyya Ta Haramta Jirgin Najeriya Shiga Kasar, Kan Cutar Corona Omicron

Best Seller Channel

Masarautar Saudiyya ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga Najeriya saboda sabon nau’in cutar Coronavirus, 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Masarautar Saudiyya ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga Najeriya saboda sabon nau’in Coronavirus, Omicron. 

A ranar Larabar da ta gabata ne wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba na cewa ana shirye-shiryen mayar da ‘yan Najeriya mazauna Masarautar kan Omicron. 

Best Seller Channel 

Sai dai wasu majiyoyi da dama a karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Kano da kuma jami’ai a filin jirgin saman Malam Aminu Kano  sun tabbatar wa Aminiya cewa an bayar da umarnin takaita zirga-zirgar jiragen sama daga Najeriya a kan Omicron. 

Tun bayan da Masarautar ta dage dokar hana zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya, mutane da dama musamman daga Kano sun je kasar don gudanar da aikin Umrah kadan, yayin da wasu ke dakon ranakun da za su ziyarta. 

Best Seller Channel 

Sai dai wani jami’in ofishin jakadancin Saudiyya da ke Kano, wanda ya zabi a sakaya sunansa saboda ba a umurce shi da ya yi magana da manema labarai ba, ya shaida wa Aminiya a ranar Laraba cewa, an bayar da umarnin takaita zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya domin duba yaduwar Omicron.

 Wani jami’i a filin tashi da saukar jiragen sama na Kano ya kuma tabbatar wa da wakilinmu cewa, tuni aka fitar da wata sanarwa cewa a soke duk wasu kananan tafiye-tafiyen Aikin Umrah, saboda wannan ci gaba. “Eh gaskiya ne domin an fitar da wata takarda cewa a soke duk wasu kananan jirage na aikin Umrah kuma ba za a kara tashi daga Najeriya ba har sai an sanar. 

Ina tsammanin suna bin matakin da wasu kasashe kamar Burtaniya suka yanke na hana kamuwa da kwayar cutar a cikin masarautar,” majiyar ta shaida wa wakilin Aminiya a cikin sirri. Sai dai daya daga cikin jiga-jigan Ma’aikatan Jirgin ya ce ba zai iya tabbatar da faruwar lamarin ba yayin da jiragen biyu Qatar da Badar Air suka bar Abuja zuwa Jeddah da safiyar Laraba. 

Best Seller Channel 

Daga baya hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Saudiyya GACA ta tabbatar da dakatar da zirga-zirgar jiragen a cikin wata ka’ida ga dukkan kamfanonin jiragen sama da ke aiki a kasar. 

Slide Up
x