KATOBARA! Hukumar Hisba Na Shirin Daura Wani Aure Da Dan China Bayan Ya Dirkawa Yarinyar Ciki Wata Shida A Kano

IMG 20230923 WA0013

Hukumar ta shirya a yau Asabar 30 Ga watan March 2024 Zata daura musu aure karfe 1 na rana bayan ya dirka mata ciki Wata 6!

Alfijir labarai ta rawaito Mal Yusuf direba shine yake tuka daya daga cikin ma aikatan kasar China Mr Shibu da ke unguwar sharada a birnin Kano.

Da farkon lamarin yar Malam Yusuf Mai suna Maryam takan je wajen Mahaifin ta a wajen aikinsa duba da basu da nisa da Kamfanin, a irin wannan zuwan ne Mr Shibu ya lallaba Maryam da sunan soyayya, ya dirka Mata ciki wata 6, kamar yadda Mahaifin Maryam da ita kanta suka tabbar mana.

Mr Shibu bayan lamarin ya bayyana ne ya bada mota aka kai Maryam wani asibiti aka yi mata allurai, amma Ciki ya ki zubewa, yarinyar kuma ta shiga galabaita.

Daga karshe ya dankawa mahaifin yarinyar Naira dubu 50 da zummar suje a zubar da ciki sannan kuma zai basu Miliyan daya.

Sun karzaya asibitin Best Choice domin a zubar musu da cikin amma likitan dake kan aiki ya tabbatar musu da cewar basa wannan aiki, kamar yadda suka tattauna da Alfijir Labarai.

A binciken da Jaridar Alfijir labarai tayi na nuna an yiwa mahaifin Maryam barazanane akan raba shi da Aikinsa mutukar ya bari zancen ya fito. Don haka yake cikin damuwa gaya, wanda hakan ta kasa bashi damar Yayi mana Cikakken bayani akan lamarin, sai dai akwai matarsa da yayansa da suka tabbatar wa da Alfijir Labarai faruwar wadannan abubuwan.

Bayan da Alfijir Labarai ta ziyarci hukumar Hisba a kano domin jin yadda aka kwana da kuma yadda za a tashi, ACG mai kula da lamarin ya tabbatar wa da Alfijir Labarai cewar an gayyato shi Mr Shibu, zuwa hukumar kuma an hada jami’an hukumar da iyayen yarinyar domin aje asibiti kan duba lafiyar Maryam.

ACG tabbatar wa da wakilin Alfijir Labarai cewar za suyi mai yuwuwa domin nemawa Maryam hakkinta, duba da mai Faruwa ta faru, An yi wannan Tattaunawar ne a ranar Lahadin data gabata.

Kwatsam sai Alfijir Labarai ta tuntubi Mal Yusuf direba a jiya Juma’a, nan yake bamu labarin cewar wai hukumar Hisbah zata daurawa yar sa Aure a yau asabar da Mr Shibu Dan Kasar China, sai nake tambayarsa dama ana Aure tsakanin kafiri da musulma, nan yace wai an ce ya musulunta, kuma ACG yace sun sanar da babban kwamanda Mal Aminu Daurawa kuma yace za a iya babu laifi, kamar yadda Mahaifin yarinyar ya sanar mana.

Alfijir labarai tayi ta kokarin jin ta bakin Mal Daurawa hakan bai samu ba, hakazalika mun tuntubi Mal Mujahid mataimakin Babban Kwamanda ta waya bai Sami dauka ba, haka mun tura masa sakon kar ta kwana shima shiru.

Don haka muke kira da mahukunta da su shigo cikin wannan lamarin domin kawo gyara cikin sa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *