Katobara! Wata Mata Ta Yanka Mijinta Sannan Kuma Ta Kone Gawar

IMG 20240730 WA0895

Daga Aminu Bala Madobi

kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya, CP Benneth C. Igweh, na fatan tabbatar da cewa za a yi adalci a lamarin.

Alfijir labarai ta rawaito a ranar Talata ne ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja da ke yankin Pegi suka kama wata matar aure mai matsakaicin shekaru bisa laifin kashe mijinta kan takaddamar rabon gado.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, “a ranar 29 ga watan Yuli, 2024, da misalin karfe 6:00 na yamma, bisa sahihan bayanan sirri, sun kama wata Rahimat Salaum, ‘yar shekaru 23 a garin Pegi, Abuja, bisa zargin kisan gilla ga mijinta.

“Wadda ake zargin tana yunkurin guduwa ne da kayan mijin, kuma rahotanni sun nuna cewa ya shafe kusan kwanaki uku a cikin wata karamar mota inda ‘yan sanda suka kama ta.

“Da aka yi ma ta tambayoyi, wadda ake zargin ta amince da kashe mijinta bayan fada ya barke a tsakaninsu. “Daga baya ta jagoranci ‘yan sandan zuwa wani gini da ba a kammala ba inda ta jefar da gawar da ta kone.

“Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya, CP Benneth C. Igweh, na fatan tabbatar da cewa za a yi adalci a lamarin domin ya bukaci mazauna yankin da su yi taka-tsan-tsan da muhallansu tare da bayar da rahoton abubuwan da ake zargi ga ‘yan sanda.

IMG 20240730 WA0889
Yan sandan Abuja

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *