Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Kwamatin Sabon Mafi Karancin Albashi Na Kasa

FB IMG 1719671782992

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamnan jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da kwamitin ba da shawara kan sabon albashin ma’aikata na kasa, sa’o’i 48 kacal bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sabon mafi karancin albashi na N70,000 kamar yadda kungiyar kwadago ta shirya.

Alfijir labarai ta ruwaito kano ita ce jiha ta farko a fadin kasar da ta kafa irin wannan kwamiti. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a yau a fadar gwamnatin jihar, wanda mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya jagoranta a madadin gwamnan.

A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, Kakakin Mataimakin Gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu, ya bayyana cewa Gwamna Yusuf ya jaddada alhakin kwamitin na tsara yadda ya kamata kan sabon mafi karancin albashin da aka amince da shi, da kuma gabatar da wata shawara mai amfani don aiwatarwa nan take.

Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa aiwatar da sabon mafi karancin albashin zai kara habaka cigaban jihar Kano a dukkanin bangarori, domin jin dadin ma’aikata shi ne abin da gwamnati ta sa gaba.

An dai dorawa kwamitin aikin bayar da sakamako cikin makonni uku. Gwamnan ya tunatar da ‘yan kwamitin cewa an zabe su bisa cancanta, ya kuma bukace su da su bayar da gamsassun sakamako.

Sabon shugaban kwamitin da aka kaddamar Alh. Usman Bala Muhammad, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin jihar ya nuna jin dadinsa ga gwamnatin jihar bisa amincewar da ta yi wa kwamitin.

Ya yi nuni da cewa atisayen zai yi matukar tasiri ga dubban ma’aikata a bangarori masu zaman kansu da na gwamnati ta hanyar daidaita muradun masu daukar ma’aikata, da ma’aikata, da kuma jama’a.

Ya ba da tabbacin cewa kwamitin zai yi amfani da cikakken bincike na bayanai tare da yin la’akari da duk abubuwan da suka dace don isa ga shawarar mafi karancin albashi ga gwamnatin jihar.

Mambobin kwamitin sun hada da:
– Alh. Usman Bala Muhammad, mai bawa gwamna shawara na musamman kan harkokin jiha (Shugaba)
– Alh. Ibrahim Jibril Fagge, Hon. Kwamishinan Kudi
– Alh. Musa Suleman Shanono, Hon. Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi
– Baba Halilu Dantiye, Hon. Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida
– Baffa Sani Gaya
– Prof. Aliyu Isa Aliyu
– Salahudeen Habib Isa
– Ibrahim I. Boyi
– Ibrahim Muhammad Kabara
– Mustapha Nuraddeen Muhammad
– Abdulkadir Abdussalam
– Umar Muhammad Jalo
– Hassan Salisu Kofar Mata
– Yahaya Umar

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *