Kotun Shari’ar Muslunci, da ke zaman ta a harabar Hukumar Hisbah a jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Alkali Sani Tanimu Sani Hausawa, ta yanke ƙwarya-ƙwaryan hukunci ga wani miji kan ya maida matarsa da su ke tare shekaru goma da su ka gabata.
Alfijir Labarai ta rawaito Mijin dai na zargin wani hakimi a jihar, wanda shi ne mahaifin matar ta sa, da ƙoƙarin kashe musu aure sakamakon mijin yar ta sa ya yi mata kishiya, inda su kuma ƴaƴan sarauta ba a yi musu kishiya.
Tun da fari, matar ce ta kai mijin nata kara zuwa kotun, inda take neman a kotu ta yanke igiyar auren na ta da mijin ta saboda ya kara aure.
A nan ne lauyan wanda ake kara, Barista Umar Yusuf Khalil, ya roki kotu da ta basu damar sulhu kasancewar sun kwashe shekaru 10 tare kuma suna da ƴaƴa huɗu.
A cewarsa, shi aure rai ne da shi sai lokacin da Allah Ya yi zai mutu, zai mutu, saboda haka su ke neman kotu ta sahale wa mijin ya mayar da matarsa, wacce ta shafe shekara ta na yaji a gidan mahaifinta.
Shi kuma lauyan mai kara, Barista Ibrahim Umar, ya shaidawa kotun, cikin yanayi na barkwanci, cewa idan wanda ake ƙara ya je yin biko, to ya tafi da daƙwalen kaji.
Sannan kuma ya musanta zargin cewa mahaifinta ne ya umarce ta da tafi gida domin gidansu na sarauta ne, kuma ba a yi wa ƴaƴan gidan kishiya.
Ya kuma nuna cewa wanda ya ke kara na samun matsala me da mai kara, inda ta gaji da zaman shi ne ta garzaya kotun don neman a raba auren.
Daga bisani kotun kuma ta amince da hakan sannan ta sanya ranar 20 ga watan Nuwamba don sake zaman shari’ar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp