Kotu ta dakatar da likitoci masu neman kwarewa shiga yajin aiki

FB IMG 1768047596196

Kotun Kwadago ta Ƙasa da ke Abuja ta bayar da umarnin wucin-gadi da ke hana mambobin ƙungiyar likitocin masu neman kwarewa ta Najeriya (NARD) shiga kowanne irin yajin aiki.

Mai shari’a E. D. Subilim, wanda ke jagorantar kotun, ya bayar da umarnin ne a ranar Juma’a, bayan wani buƙatar gaggawa (ex parte) da gwamnatin tarayya tare da Antoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi, suka shigar.

Gwamnatin tarayya ta shigar da ƙarar ne a kan NARD, shugabanta na ƙasa Mohammad Usman Suleman, da kuma sakatarenta na ƙasa Shuaibu Ibrahim.

Tun da farko, ƙungiyar ta sanar da cewa mambobinta za su shiga yajin aiki daga ranar 12 ga Janairu, sakamakon gazawar gwamnati wajen warware buƙatun ta na aiki da na ƙwarewa da likitocin suka dade suna nema.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *