Kotu Ta Daure Wani Magidanci shekaru 19 Kan Laifin Yiwa Ƙaramar Yarinya Fyade

Kotu

Babbar Kotun jihar Kano mai lamba 1 da ke Sakatariyar Audu Bako, Karkashin mai shari’a babbar alakaliyar jahar Kano Dije Abdu Aboki, ta yanke wa wani magidanci Ado Idris, hukuncin daurin shekaru 19, sakamakon samunsa da yiwa wata karamar yarinya fyade a unguwar Fagge.

Alfijir labarai ta rawaito Barista Fatima Ado Ahmad mai gabatar da kara kuma lauyar gwamnati ta gabatarwa da Kotun shaidu biyar, shi kuma wanda ake tuhuma ya kare kansa.

Mai shari’a ta yi dogon nazari da bin diddigi aka lamarin, inda ta yanke wa wanda aka tuhuma Ado Idris hukuncin daurin shekaru 19 a gidan gyaran hali

Wanda ake zargin dai kotun ta kama shi da laifin lalata da wata yarinya a mabanbantan lokuta.

Gani ga wane dai ya isa wane tsoron Allah

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *