Kotu Ta Karɓe Gidan Shugaban Kamfanin Al Khashafi Travel Kan Badakalar Miliyan 535

Alfijr ta rawaito wata kotu da ke zaman ta a Kano Miller Road ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Maryam A Sabo ta karbe wani Katafaren gida mallakar Sadat Shehu Idris mai kamfanin Al Khashafi travel & tour

Hakan ya biyo bayan karya yarjejeniya da ya dauka a gaban mai shari’a, na dawo wa da kamfanin Khaleel Travel & Tours da AL Ansar Travel & Tours Kudadensu a ƙasar Saudiyya, tsawon wata 7 amma hakan ya gagara.

Idan Zaku iya tunawa tun a 1st Nuwamba 2022 kamfanonin
Khaleel Travel & Tours da AL Ansar Travel & Tours da suka shiga aikin Hajjin shekarar 2022 da aka kammala, sun kai kara zuwa karamin ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar Saudiyya, kan rashin biyan bizar tafiya, tikitin jirgi da otal. masaukin da aka biya wani kamfanin tafiye tafiyen na Saudiyya mai suna Alkahasafi Travel Tours Limited da Alshamel International Limited Company.

Kamfanonin sun bukaci kamfanonin kasar Saudiyya da su maido da kudaden da suka kai sama da Naira miliyan 535 da aka biya a asusunsu domin yin hidima a lokacin, aikin Hajjin 2022, wanda shugaban kamfanin Al Kashafi Travel & Tours da ke Kano ya ke tsani

Mai shari’a ta dage zaman zuwa lokaci na gaba, don haka idan suka ci gaba da wasa da hankalin Kotu, za a dau mataki na gaba akan sa da gidan nasa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *