Kotu Ta Tura Shugaban Karamar Hukuma Gidan Gyaran hali Kan Zargin Kisan Kai

Screenshot 20221202 154709 com.facebook.katana edit 16234138425645


Kotu ta tasa ƙeyar shugaban ƙaramar hukumar Ɓatagarawa kan zargin kisan kai

Alfijir labarai ta rawaito Kotun majistare da ke zamanta a Katsina ta tasa keyar shugaban karamar hukumar Batagarawa a jihar Katsina Alhaji Bala Garba Tsanni zuwa gidan yari bisa zargin kisan kai da garkuwa da mutum.

Shugaban ƙaramar hukumar da wasu mutane 11 sun gurfana a gaban kotu a karkashin sashe na 59, 249 da 189 na dokokin jihar Katsina.

Ana tuhumar su ne da laifin kashe maigarin kauyen Dabaibayawa da ke karamar hukumar Batagarawa ta jihar Katsina, Marigayi Alhaji Dikko Ahmed.

Tun da farko Alkalin Kotun Mai shari’a Abdulkarim A. Umar ya umarci ‘yan sanda da su gabatar da wadanda ake zargin a gaban kotu a ranar 25 ga watan Janairun 2024.

Sauran mutane 11 da ake tuhuma dai sun kasance a gidan yari tsawon watanni shida da suka gabata yayin da shugaban ke zaman beli a tsawon lokacin.

Da take gabatar da wanda ake tuhuma a kotu a ranar Alhamis, ’yan sandan sun ce sun kammala bincike kan lamarin.

Hakan ya sa babban alkalin kotun ya ba da umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan yari har zuwa ranar 7 ga watan Match 2024.

Katsina Post

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *