Kotu ta Umarci a Kamo Mata Wani Jami’in Kwastam A Kano

FB IMG 1662410415944

Babbar kotun shari’ar musulunci dake zaman ta a sabon gari a jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari’ah, Hamza Garba Malafa ta yi umarnin a kamo mata wani jami’in costom, mai suna Yusuf Isma’il Muktar Mai biscuits. Biyo bayan kin bayyana a kotun a yau Alhamis.

Alfijir labarai ta rawaito tun da fari dai wani maraya ne mai suna Abdullahi Shehu Aliyu wanda aka fi sani da baballe, ya yi karar sa kan cewa yana kokarin kwace masa wani katon kango, dake Kawaji layout a Karamar hukumar Nasarawa.

Rahotanni sun bayyana cewa kimar kango ta kai Naira miliyan hamsin. Wanda ya siya a wajan yayan Yusuf din mai suna Mustapha Isma’il Mai biscuits. Watanni uku da suka gabata.

Kan haka ne lauyan Mai kara Saleh Idris Bello ya yi roko a kamo shi, tin da dai an bashi sammaci amma bai je kotun ba.

Tuni dai alƙalin kotun mai shari’a Hamza Garba ta amince da rokon lauyan masu kara, Inda yace a kamo Yusuf Isma’el Nan da ranar 8/01/23.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *