Kotu ta umarci Aminu Ado ya daina ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano

FB IMG 1716833360872

Babbar kotun jihar kano ta umarci sarkin Kano na 15, Mai martaba Aminu Ado bayero da ya daina kira ko gabatar da kansa a matsayin Sarkin Kano.

Alfijir ta rawaito kotun ta bayar da umarni ga ƴansanda da su fitar da shi daga fadar Sarkin Kano da ke unguwar Nassarawa a cikin jihar.

A umarnin da kotun ta bayar bayan da ta karanta bukatar da lauyan gwamnatin jihar Kanon Ibrahim Isa Wangida ya gabatar mata, kotun ta zartar da umarnin na wucin-gadi.

Bayan Alhaji Aminu Ado Bayero, kotun ta kuma umarci sauran sarakuna hudu da aka rushe da su daina ayyana kansu a matsayin sarakunan masarautun.

Masarautun da aka rushe dai su ne wadda tsohuwar gwamnatin jihar kanon ta APC karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta kirkiro wato Kano da Bichi da Gaya da Rano da kuma Karaye.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Sarkin na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya gabatar da zaman fada a yau Litinin.

Babbar kotun ta dage zaman sauraren karar wadda aka shigar a gabanta ranar 24 ga watan nan na Mayu 2024, zuwa ranar 11 ga watan Yuni shekara ta 2024 domin saurare.

IMG 20240527 WA0234
Order
IMG 20240527 WA0233
Order

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/F9mRRuOf58G3MlLKsNCJbL

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *