Wata babbar kotu dake zamanta a jihar Kano ta yanke wa wasu `yan bijilanti biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta samesu da laifin kisan wani matashi mai shekara 17.
Alfijir labarai ta rawaito Jami an bajilantin sun aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Janairun 2022.
‘Yan bijilantin, waɗanda suke aiki a cibiyar bunƙasa rayuwar matasa ta Sani Abacha da ke kan hanyar Madobi, sun haɗa da Emmanuel Korau da Elisha Ayuba da Irimiya Timothy da Auwalu Jafar da kuma Mustapha Haladu.
Lauyan Masu kara Barrister Lamido Soron Dinki, gabannin yanke hukuncin ya shaida wa kotun cewa waÉ—anda ake zargi sun kama matashin ne a sabon titi, Panshekara, inda suka far masa da duka da da sanduna, Wanda daga bisani suka raunata shi ta hanyar caka masa wuka, sannan suka ja shi a kasa suka jefa shi cikin babur din adaidaita sahu, lamarin da ya yai sanadin mutuwarsa.
Lauyan waɗanda aka yi ƙarar ya yi ƙokarin kare su, inda ya bayyana cewa sun je ne da nufin kama matashin ba halaka shi ba, bayan an kai musu karan sa.
Sai dai, kamar yadda mai magana da yawun kotunan jihar Kano, Malam Baba Jibo Ibrahim ya ce, mai shara`a Dije Aboki ta yanke wa `yan bangan hukunci ne bayan ta gamsu da hujjojin da mai gabatar da ƙarar ya gabatar:
Sai dai kuma mutanen da aka yanke wa hukuncin na da damar ɗaukaka ƙara.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V