Kotu Ta Yankewa Aisha Mama Boko Haram Hukuncin Ɗaurin Shekaru 10

Alfijr ta rawaito an yankewa Aisha Alkali Wakil, wacce aka fi sani da Mama Boko Haram hukuncin, bisa samunta da laifin zamba.

Mai shari’a Aisha Kumaliya ta babbar kotun jihar Borno da ke zamanta a Maiduguri a ranar Laraba, 21 ga watan Disamba, 2022, tare da Tahiru Saidu Daura, da Yarima Lawal, ta yanke wa Mama Boko Haram hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari bisa samun su da laifin hada baki, zamba, da kuma samun N120.
500,000.00 ta hanyar yaudara.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ce, ta gurfanar da wadanda ake tuhumar a ranar Laraba, 8 ga watan Disamba, 2021, bisa tuhume-tuhume biyar.

Mai shari’a Kumaliya ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhumar da ake yi wa wadanda ake tuhumar ba tare da wata shakka ba.

“Kotu ta same ku Aisha Alkali Wakil, Tahiru Alhaji Saidu Daura, Yarima Lawal Shoyade da laifi kuma ta same ku da laifin da ake tuhumar ku.”

Mai shari’a Kumaliya ta yanke musu hukuncin daurin shekaru bakwai a kan tuhume-tuhume na farko.

A tuhume-tuhume na uku, Alkalin ya yanke wa wadanda ake tuhuma hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari.

Jumullar shekarun za su gudana a lokaci guda.

Alkalin kotun ta umurci wadanda aka yankewa hukuncin tare da mayar da kudaden da suka kai N66m ga wanda ya shigar da kara ko kuma su kara zaman gidan yari na tsawon shekaru bakwai.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *