Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Yi Watsi Da Ƙarar Jam’iyyar NNPP Kan Alhassan Doguwa

Alfijr ta rawaito Kotun daukaka kara da ke Kano a ranar Juma’a ta yi fatali da karar da jam’iyyar New Nigeria People’s Party da dan takararta Salisu Yushau suka shigar, kan sake zaben Alhassan Doguwa na jam’iyyar APC.

Kwamitin mutum uku karkashin jagorancin Mai shari’a Ita George-Mbaba, a cikin hukuncin da aka yanke, ya kuma yi watsi da karar na rashin hurumin shari’a tare da tabbatar da hukuncin da kotun ta yanke.

Kotun dai ta amince da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta kasa da ta Jiha ta yanke.

George-Mbaba ya kuma yi watsi da rokon da masu daukaka kara suka yi na hana Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) takardar shaidar cin zabe ga Doguwa tare da janye takardar shedar da ta riga ta ba shi.

Alkalin ya kuma umurci masu kara da su biya wadanda ake karan kudi Naira 200,000 a matsayin kudin shigar da kara.

Wadanda suka shigar da kara a cikin bukatar tasu sun bukaci kotun da ta ajiye zaben ranar 15 ga watan Afrilu wanda ya bayyana Mista Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Tudun Wada/ Doguwa ta tarayya.

Wadanda ake kara su ne: Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), Alhassan Doguwa, mamba mai wakiltar Tudun Wada/ Doguwa Tarayya Kano da APC.

Tun da farko, Lauyan wadanda suka shigar da kara, Adegboyega Awomolo, SAN, ya bayar da hujjar cewa sashe na 4 (6) na dokar zabe ta 2022 ya ba da ikon cewa kowace jam’iyya za ta iya kalubalantar hukuncin da INEC ta yanke, inda ya kara da cewa daukaka karar ta biyo bayan tanadin dokar zabe.

Ya bukaci kotun da ta ba da damar daukaka karar sannan ta yi fatali da rashin amincewar wadanda ake kara na farko.

Lauyan wanda ake kara na farko, Idris Yakubu, ya bukaci kotun da ta yi watsi da karar.

Lauyan wadanda ake kara na biyu da na uku, Nureini Jimoh da Abdul Adamu-Fagge, sun bukaci kotun da ta yi watsi da babbar karar da aka shigar a gaban kotun tare da yin watsi da daukaka karar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *