Kotun Musulunci ta Umarci Choci a Kano ta Rantsar da Wani Kirista da Littafin Bible.

Bible

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu Karkashin Mai Shari Ibrahim Sarki Yola, ya ummarci wata Chochi data rantsar da wani Kirista Mai suna Yakubu Tumoti da littafin baibul domin kaucewa zargin da wani matashi yayi masa cewa sun bashi ajiyar mashin mai kafa 2 lifan ansace.

Tunda farko dai matashin mai suna Mahmud Yusuf Kofar Nasarawa ya shigar da kara kotu ta kwato masa Mashin dinsa da Yaje magaji Rumfa domin yin Booking na filin Bal da zasuyi.

Anan suka tambayi Tumoti inda zasu ajiye mashin din nasu kuma anan take ya nuna musu sai dai bayan ajiyewar sun dawo daukar sukaga babu nasu awajen ko da suka tambaye shi sai yace yaga wasu wai sun tura sun give dashi.

Ko da mai Shari Ibrahim Sarki Yola ya numfasa ya mai da tambaya ga Wanda ake zargi Tumoti sai yace shi Sam basu bashi wani ajiyar mashin ba hasalima shi bai taba ganin suba tunda shi aikin sa awajan yabude Gate ashigo ko afita.

Alfijir Labarai ta rawaito tuni mai Shari a ya tambayi Tumoti cewa a matsayin sa na Kirista koya yadda ayi masa Shari’a anan Kotun ta Musulunci ko a kai su Magistrate.

Kuma nan take Yakubu Tumoti ya yaroki da ayi masa Shari’ar anan. Wanda hakan Sarki Yola ya ummarci Inspector Sulaiman daya daga cikin ma aikatan kotu da Rijistara da suje da Tumoti Chochin da yake gabatar da ibadar sa da Babban malamin sa yarantsar da shi kan cewa bashi ne ya dauki Babur din ba kuma Baisan Wanda ya dauka ba Kuma ba a hada kai dashi an daukaba kuma hasalima bai sansuba.

Mai Shari Ibrahim Sarki Yola ya dage cigaba da shari’ar zuwa ranar 4 gawatan 12.

Arewa Radio

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *