Kotunan Najeriya za su fara gudanar shari’a ta intanet

Ma’aikatar shari’ar ta Najeriya ta ƙaddamar da wani sabon tsari da zai bai wa kotuna damar sauraron shari’o’i daga nesa ta hanyar amfani da intanet

Best Seller Channel 

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce tsarin zai taimaka wajen rage cunkoso a gidajen yari, da kuma kare waɗanda ake tsare da su, har ma da jami’an tsaron gidajen yari daga afkawa hannun miyagun mutane da kuma saboda kararowar annobar korona.

BBC ta rawaito Abubakar Malami, ministan shari’a na Najeriya ne ya kaddamar da wannan sabon tsarin, inda aka fara misali da gidan gyara hali na Kuje da ke Abuja babban birnin kasar

Kakakin Yada labarai da hulda da jama a na ma aikata Sharia Dakta Umar Jibrilu Gwandu, ya ce wannan tsarin zai kawar da jinkiri wajen gudanar da shari’o’i a fadin kasar da zarar an kaddamar da shi. 


Best Seller Channel 

Ya kuma kara da cewa tsarin zai rage yawan kaikawo da ake yi da wadanda ake tuhuma da aikata laifuka daga gidajen yari zuwa kotuna, ciki har da lauyoyi da sauran ma’aikata. 


Best Seller Channel 

Dakta Umar Jibrilu Gwandu ya ce wannan sabon tsarin ya yi daidai da tanade-tanaden tsarin mulkin Najeriya: “Sashe na 36, karamin sashe na 3 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce a saurari dukkan shari’o’o a bainar jama’a ba tare da boye-boye ba.”

Best Seller Channel 

Da fatan wannan yunkurin da  gwamnatin Nigeria tayi zai haifar da da mai ido, Kuma ya kawo Karshen cin koso a gidajen yarin kasar nan.