Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yarda cewa yana cikin zanga-zangar daban-daban a shekarun baya amma ba tare da tashin hankali ba.
Alfijir labarai ta ruwaito shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi takardar amincewa daga sabon jakadan Amurka a Najeriya, Mista Richard Mills Jr. a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Tinubu ya jaddada muhimmancin dorewar dimokuradiyya da kuma turakun ta, yana mai cewa zanga-zanga wani bangare ne na dimokuradiyya, amma babu wata gwamnati da za ta amince da zanga-zangar da ke janyo asarar rayuka da dukiyoyi.
“A lokacin soji, mun yi ta rajin nuna adawa da mulkin kama-karya, kuma ina cikin kungiyar da suka gudanar da zanga-zangar lumana ba tare da yin barna ba. Mun yi aiki tukuru domin tabbatar da shekaru 25 na mulkin dimokuradiyya ba tare da mishkila ba, kuma zan ci gaba da raya hmm wannan dimokuradiyya.”
“Muna sa ran Najeriya da Amurka za su ci gaba da yin aiki don fadada hadin gwiwa a kan manufofi guda da dabi’un dimokradiyya,” in ji Tinubu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj