Kungiyar Yarabawa Ta ja Kunnan Shugaba Tinubu Kan Batun Dakatar Da Shirin Yin Zanga-zanga

Screenshot 20240725 221902 Chrome

Kungiyar yarabawa ta Afenifere taja kunnan Shugaban  kasa bola tinubu Kan batun dakatar da Shirin yin zanga zanga sabida san zuciya da munanan manufa

Alfijir labarai ta ruwaito da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise TV a ranar Alhamis mai magana da yawun kungiyar ta Afenifere Justice Faloye ya bayyana cewa, kungiyar ta gargadi shugaba Bola Tinubu kan sakamakon aiwatar da munanan manufofinsa na tattalin arziki da ba su da inganci, wadanda suka jefa miliyoyin yan Najeriya cikin matsin rayuwa da talauci

Ba muna tada hankalin muba, amma mun fahimci cewa akwai zanga-zangar da ke tafe, kuma mun fahimci cewa hakan  ya faru ne saboda yunwar da ake fama da ita a kasar nan, kuma munyi  gargadin cewa ba ma son tashin hankali. Ba mu san shugabannin da zasu hana goyon bayan zanga-zangar,” in ji kakakin Afenifere.

Faloye ya gargadi Tinubu game da illar da ke tattare da cire tallafin man fetur, amma yana da tabbacin zai iya zuwa inda babu wata gwamnati da ta je.

Ya kara da cewa, ba wadanda ke zanga-zangar ko kuma masu son yin zanga-zanga ne ke kawo barazana ga harkokin siyasa ba.

“Ba za ku iya cire tallafin irin wannan a ko’ina ba, ko da a Ingila da Amurka ko kasashe masu arziki a duniya. Idan ka cire tallafin a Ingila a yau, nan da makonni biyu, za ka ga irin wannan zanga-zangar ta fito. Don haka, a gare mu mu ce mutane su ci gaba da jin yunwa, rashin adalci ne. ” in ji shi.

Da aka tambaye shi ko ba ya goyon bayan Tinubu kuma idan yana tunanin shugaban kasa ya gaza wa jama’a, Faloye ya ce, “Tabbas, mun yi imanin cewa Shugaban zai yi mana adalci sama-sama.

Ya kuma yi Kira da Bola Tinubu daya sake fasalin tattalin arziki. Muna da tattalin arzikin tun a lokacin mulkin mallaka”.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *