Kukan Kurciya! Kakar Zabe Ta 2023 Ta Kama!

DAGA
MUDASSIR ALIYU YUNUSA.

FASSARA: YUSUF ABBA SARKI.

A duk bayan shekara hudu a Najeriya a ke sake sabon zubi na masu rike da madafun iko, wanda ‘Yan kasa ke taza da tsifar wanda suka bawa amanar jagorantarsu.

Tuni lokaci ya kurewa wadanda aka zabe su a kakar zabe da ta gabata wato 2019. Kuma hukumar zabe ta kasa ta shirya tsaf domin gudanar da zabe.

Zabe shike tabbatar da dorewar Dimokradiya musanman a kasashe irin namu, wanda juyin mulki ya zama ruwan dare, Alal misali a Najeriya Sojoji sun yi shekaru 29 suna mulkin tun daga samun ‘yancin kai.

Kafin zabe ya zama Mai inganci kuma karbabbe, dole Sai ya barranta daga duk wani hargitsi da dabanci da tada zaune tsaye da murdiya da kuma magudi, duk domin a bawa jama’a dama su iya tantance wanda ya kamata su dangwala kuri’arsu, musanman ta fuskar Nagarta, amintacce, yardajje, lafiyayye, gogagge, bugu da kari kuma wanda aka bibiyi tarihinsa bashi da tabo na almundahana ko wani aibu a rayuwarsa ko mukamin da ya rike a baya.

Haka zalika ‘Yan dangwale dole su guji zabar Yan siyasar da suke hakikancewa Sai sun ci zabe ko ta halin kaka. Hakika mun dai ga zamuna daban daban na’ Yan siyasa da masu azurta kawunansu, da masu daga mu Sai Yan kungiyarmu ko abokansu da masu wawure arzikin al’ummarsu, to mun dai ga darasi iri-iri kuma mun dandana kudarmu, ya rage gare mu, mu taje mu tsefe duk wani Dan takara da bai dace da kasarmu ko jaharmu ba.

Abun da nake kara jaddadawa shi ne masu kada kuri’a su tabbatar sun bi diddigin kowanne Dan takarar da yake so a zabe shi ko a sake zabarsa, me ya yiwa mutanensa a baya kafin a dangwala masa kuri’a.

Sai a duba taya zai iya amfanar al’umma. Al’adar Yan siyasa yin zakin baki da tausasa harshe da yin alkawarika masu dadi, su yaudari al’umma duk domin samun yardar su, wasu kan canja kamanninsu wajen rikidewa su koma mutanen kirki Don a amince musu.

A zance na gaskiya idan muna so mu ‘yanto kanmu daga hannun gurbatattun Yan siyasa dole mu lura sosai wajen gano nagartattun Yan takara masu rufe Kura da fatar Akuya.

Yana da kyau mu kalli mutumin da zai iya magance mana matsalolin mu, wanda zai yaki mugun talaucin da yayi mana dabaibayi, wanda zai yaki cin hanci da rashawa daga tushe, wanda zai magance rashin aikin yi da yake haifar mana da tabarbarewar tsaro, wanda zai fi fita maslahar al’umma fiye da maslahar kansa da ta iyalensa, kuma wanda zai yiwa mutane aikin da suke bukata ba wanda yake so ba.

Dole kafin mu kada kuri’a mu bawa kanmu amsoshin wadannan tambayoyi.

Shin Dan takarar nan zai bautawa mutanen sa ne tsakanin da Allah ko kuwa zai bautawa son zuciyar sa ne?

Shin yana da zakuwa da jajircewa ya ga walwalar mutanen sa komai wuya komai rintsi?

Yana da sha’awar ci gaban mutanensa da kasa baki daya? Yana da juriyar fuskantar kowanne kalubale da zai dakusar da ci gaban kasa?

A cikin wadannan Yan takarar wanne kake kanin a karkashin sa Yan kasa zasu Sharbi romon Dimokradiya?

In dai muna so mu tsaftace siyasar nan Sai mun ga wa zai dace da wannan kucerar mulkin. Duk da kalubale na tsananin rayuwa da ake ciki.

Ina bawa juna shawara mu kiyayi sayar da Yancinmu ta hanyar bada kudi, ko kayan abinci, wanda adashi ne suka zuba zasu kwashe bayan sun dare karagar mulki, mu Kuma mu dauwama cikin Fatara da yunwa mu zama karnukan Yan siyasa muna musu roko da banbadanci duk da tsananin jiran layin zabar su cikin zafin rana, sanyi ko ruwa da iska.

Ya ‘Yan uwa Yan Najeriya mu karkade kuri’armu lokaci yayi da zamu yi tsayin daka wajen daidaita kasarmu ta koma kan tafarki madaidaici.

Mu duba nauyin da yake kan kowacce kujerar siyasa Don musan wa zamu dora a kai. Mu tuna ana yin zabe ne a rana daya kacal, amma wa’adinsa shekara hudu ne, yana da kyau muyi amfani da wannan damar kar muyi kuskuren da zai samu nadamar shekara hudu.

Kuri’armu ita ce Yancinmu! Dole mu zabi yardajjun mutane adalai! Idan ko ba haka ba mudandana kudar mu, ta yunwa da fatara da rashin kwanciyar hankali a kasar mu ta gado!

Daga karshe Ina fata ayi zabe na gaskiya babu hamaiya, fata na mu samu shugabanni nagartattu, adalai wadanda suke shirye su dauki dukkan dawainiyarmu!

-Mudassir zaku iya tuntuba ta a 👉mudassiray@gmail.com

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *