Kungiyar Ƙwadago ta karyata batun sanarwar fara yajin aikin a Nigeria

FB IMG 1702828536857

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta yi watsi da wata sanarwar shiga yajin aikin da ake zargin ta shirya yi a ranar Litinin.

Alfijir labarai ta rawaito Mista Benson Upah, shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NLC ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja

Akwai wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar ta NLC da kuma babban sakataren kungiyar TUC, Emmanuel Ugboaja da Nuhu Toro, na cewa za a fara yajin aikin a fadin kasar a ranar Litinin mai zuwa.

A cewar Upa, maganar karya ce kuma babu sanarwar yajin aiki daga gare mu.

“Muna so mu tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa wannan sanarwar ba ta fito daga gare mu ba, kuma ba mu da niyyar fara wani yajin aiki a wannan lokacin,” in ji shi.

Ya ce an shawarci ‘yan Najeriya da abin ya shafa da su yi watsi da sanarwar kuma su dauke ta a matsayin ta bogi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *