Alfijr
Kungiyar Dillalan Man fetur ta Ƙasa, IPMAN ta janye matsayarta ta sayar da litar mai daga naira 180 zuwa sama.
IPMAN ta ce za ta hakura ta ci gaba da sayar da shi a kan farashin gwamnati na naira 165.
Alfijr
A ganawa da manema labarai a jiya Laraba a Abuja, Shugaban ƙungiyar, Chinedu Okoronkwo ya ce hukumar PPMC ta amsa za ta biya musu bukatun da su ka gabatar.
A kan haka ya bukaci ƴan ƙasa da su daina fargabar fuskantar karancin man fetur a gidajen mai, inda ya ce yanzu haka akwai isashshen mai a ƙasa.
Okoronkwo ya ƙara da cewa yanzu haka ana loda man daga Legas zuwa sauran yankunan kasar, kuma yana sa ran nan gaba kadan za a daina dogayen layuka a gidajen man a fadin kasar.
Alfijr
A makon nan ne dai IPMAN, reshen jihar Lagos ta bayyana cewa ba za ta iya sayar da mai kasa da naira 180 a duk lita, bayan da ta ce yanayin yadda take kashe kudi kafin sauke man a gidaje ya karu sosai.
Kamar yadda Daily Nigerian Hausa Ta Wallafa