Haɗakar ƙungiyoyin ma’aikatan ɓangaren lafiya, JOHESU, ta fara yajin aikin ƙasa baki ɗaya a yau, Asabar 15 ga Nuwamba.
Kungiyar ta ce gwamnati ta gaza aiwatar da gyare-gyare a tsarin biyan albashin ma’aikatanta na tsawon shekaru 12, ciki har da albashi ƙarƙashin tsarin CONHESS, alawus-alawus, da yanayin walwala da jin daɗin ma’aikata.
Shugaban kungiyar, Kwamred Kabiru Ado Minjibir, ya ce yajin aikin ya zama dole domin tilastawa gwamnati daukar matakin da ya dace.
Hakan ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ke gudanar da nata yajin aikin a fadin ƙasar.
Yaya kuke kallon yadda bangaren lafiya ke yawan barazanar tafiya Yajin aiki a kasar?
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t