Kungiyar Matasan Arewa Ta Aikewa Da Shugaban Majalisar Dattawa Budaddiyar Wasika Akan Sanata Ningi

IMG 20240314 142533

Kungiyar Matasan Arewa Ta bada Kwanaki Uku A janye Dakatarwar da aka yiwa Sen Abdul Ningi Ko Kuma Su shiga Zanga-zanga A Jihohin 19 da suke Arewacin Najeriya.

Matasan Arewa Sun Yi Barazanar shiga Zanga-zangar ko kuma Shugaban majalisar Akpabio ya gaggauta soke matakin da ya ɗauka na dakatar da Sen Ningi saboda Yayi zargin anyi chushen Naira Tiriliyan 3 a cikin Kasafin Kuɗin na 2024.

A ƙarƙashin kungiyar matasan Arewa masu fafutukar Ganin an Gudanar da Shugabanci nagari sunyi Allah-wadai da matakin dakatar da Sanata Abdul Ahmed Ningi na mazabar Bauchi ta tsakiya, Wanda kuma ya riƙe muƙamin Shugaban kungiyar Sanatocin Arewa na Majalisar Dattawa ta 10 Kafin yayi murabus kwanaki biyu da suka Gabata.

A Cikin wata sanarwar manema labarai da suka fitar A Yau Alhamis Kakakin kungiyar, Kwamared Abdul Danbature, ya bayyana cewa matakin da Sanata Abdul Ningi ya ɗauka na tofa albarkacin bakinsa kan batun kasafin kudin Najeriya, lamarin dake cigaba da tabarbarewa a harkokin kasafin Kudin Najeriya, ya kamata a yaba masa maimakon a hukunta shi.

Sanarwar ta ‘yan jaridun ta jaddada cewa zargin da ake yiwa kasafin kudin ba sabon abu bane, Don haka bai kamata a dakatar da Sanata ba, Musamman a irin wannan mawuyacin lokaci a tarihin kasar nan. Kamar yadda sanarwar tayi nuni da cewa, zata hana daukacin gundumar Sanata wakilci a zauren majalisar na tsawon lokacin dakatarwar.

Wasu Sanatoci a yayin zaman sun nuna karara cewa akwai dalilai na siyasa a matakin karshe, Don haka muna kira ga Shugaban Majalisar Dattawa da Manyan Sanatoci dasu sake duba lamarin tare da soke dokar Dakatar da Sanata Abdul Ahmed Ningi,” inji sanarwar.

Kungiyar matasan Arewa ta cigaba da bayyana a cikin sanarwar da ta fitar cewa, idan har Shugaban Majalisar Dattawa da Majalisar Dattawa suka ki amsa kiran da suka yi na a janye dokar dakatarwar nan da kwanaki bakwai masu zuwa, Kungiyar zata tara dubban matasa a fadin Jihohin 19 na Arewa. Najeriya zata gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a fadin Jihohin kasar tare da mamaye harabar majalisar dokokin kasar nan ba da dadewa ba.

Kungiyar ta kuma yi kira ga daukacin Sanatocin Arewa dasu nemi a janye dakatarwar, Tare da bayyana illolin da hakan zai haifar ga daukacin yan Najeriya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *