Kungiyar Tubanbun Yan Daba Sun Bukaci Gwamnatin Kano Ta Gaggawa Cika alkawuran Da Ta Dauka A Kansu

IMG 214652 22126 1769114845984

Shugabannin kungiyar tubabbun ’yan daba da suka ajiye makamansu a karkashin shirin Safe Corridor na Jihar Kano sun bayyana damuwarsu kan abin da suka kira jinkiri da gazawar gwamnati wajen cika alkawuran da aka dauka na gyara da inganta rayuwarsu.

Tubanbun sun ce tun bayan mika wuya da ajiye makamansu tare da mika su ga rundunar ’yan sandan Jihar Kano domin tantancewa karkashin kulawar kwamishinan Yaɗa labarai da harkokin cikin gida, camarade Ibrahim Abdullahi Waiya, har yanzu ba su samu wani gagarumin tallafi ko tsari na musamman daga gwamnati ba.

A cewarsu, shirin Safe Corridor ya zo ne da alkawuran samar musu da hanyoyin dogaro da kai, horo na koyon sana’o’i, da kuma mayar da wasu daga cikinsu makarantu, domin inganta rayuwarsu da kuma hana su komawa tsofaffin dabi’un daba da aikata laifuka.

Sun yi gargadin cewa ci gaba da jinkirta aiwatar da wadannan alkawura na iya kawo cikas ga nasarar shirin, musamman ganin halin matsin tattalin arziki da yawancin matasan ke fuskanta, wanda ka iya janyo wasu su koma harkokin laifi idan ba a dauki matakin gaggawa ba.

Da yake jawabi a madadin kungiyar tubabbun ’yan daba ta Karamar Hukumar Birni, shugabansu Salisu Inuwa Angai ya ce, cika alkawuran gwamnati zai taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen ayyukan daba a fadin Jihar Kano.

Ya bayyana cewa ingantaccen shirin gyara, koyon sana’a da ilimi ba kawai zai samar da zaman lafiya mai dorewa ba, har ma zai karfafa gwiwar sauran matasan da ke cikin harkokin daba su ajiye makamansu su rungumi zaman lafiya.

Kungiyar ta bukaci Gwamnatin Jihar Kano da ta dauki matakin gaggawa wajen cika alkawuran da ta dauka, tana mai jaddada cewa dorewar zaman lafiya da tsaron al’umma ya rataya ne kan sahihanci da cikakken aiwatar da shirye-shiryen gyara da sake shigar da matasa cikin al’umma.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *